Minene Banbancin Email da Gmail

 


Shin Menene Banbancin Email da Gmail..?

Nasan da yawan dalibai suna buqatar sanin banbancin su, da yawan mutane suna tambayar shin menene banbacin Email da Gmail, ko jiya sai da wani dan'uwa ya min wannan tambayar, dan haka yau zanyi maku bayani dalla-dalla in sha Allah.


Mutane da yawa suna rikicewa ta yadda basa gane me ake nufi idan akace Email ko suka ji ance Gmail duk a tunanin wasu da yawa abune mabanbanta wanda har ta kaiga suna rudewa, musamman ta hanyar kamance-ceniyar sunakin guda biyu, toh yau dai kam bari na ďanyi karambani da muka saba sbd ta yiwu akwai wanda abun yake shige masa duhu

MENENE EMAIL ADDRESS?

Email Address hanyace na tura saqonni daga nisan duniya zuwa ko ina ta hanyar yanar gizo-gizo wato internet, misalin abunda ake turawa ta hanyar email shine documents, wasika, PDF Files da sauran muhimman abubuwa..


MENENE GMAIL?

Gmail ďaya ne daga "Providers Internet Networks" da suke baka damar ka isar da saqonninka ta hanyar internet wanda shi Gmail manhaja ce (Software) wanda kamfanin google suka samar da shi..

Bayan Gmail akwai kamfanoni da yawa wanda basu shahara ba amma suma aikinsu duk daya ne kamar dai yadda Gmail zasu isar maka da saqonka ta hanyar Internet to su ma hakan take amma gaskiya ba kowa bane ya sansu amma suna nan suna exist, zaka iya bude Email address dinka da wadannan providers din.. ga kadan daga cikinsu.

1 Yahoomail

2 Hotmail

3 Outlook

4 Icloudmail  (wannan na masu Apple phone ne)

5 Aolmail

6 Zohomail

7 Gmxmail

8 Yendexmail

9 Mail.com

10 Iycos.com

Duk wadannan providers ne da ake iya amfani da su ta hanyar tura saqonnin "mail" zuwa ko ina a duniya darajar "Gmail" bata dara tasu da komai ba face shahara a idon duniya da qarfin jari..

Bari kuji; Idan kaji an kira Gmail kamar dai Misalin MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE Da Sauran Kamfanonin sadarawa na kira a bangaren wayar hannu kenan, to shima dai gmail daya ne daga cikin wadancan kamfanoni da suke isar da saqon mail amma ta hanyar yanar gizo-gizo haka kuma sauran kamfanoni. Following dutsicommunication.blogspot.com domin kara ilimi

Comments

Popular posts from this blog

How to Enter Text

How to format Text Font