SHIRIN TALLAFAWA YARA MATA AKAN ILIMI DA DOGARO DA KAI
SHIRIN TALLAFAWA YARA MATA AKAN ILIMI DA DOGARO DA KAI (AGILE AF PROJECT-ZAMFARA) YA JINJINA WA GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA AKAN KULAWAR DA TA NUNA GAME DA ILIMIN YAYA MATA
Sabon shirin tallafawa Ƴaƴa mata a Jahar Zamfara a ɓangaren ilimi da dogaro da kai wanda ke ƙarƙashin kulawar Bankin Duniya (AGILE AF Project-Zamfara) ya yaba wa Gwamnan Jahar Zamfara, Dr Dauda Lawal akan yadda ya nuna cikakkiyar kulawa kuma a aikace wajen inganta sha'anin Ilimi a Jahar.
Shugabar Gudanarwar Shirin ta Jahar Zamfara, Hajiya Sa'adatu Abdu Gusau ce ta yi wannan yabo jim kaɗan bayan da ta gabatar da dukkan takardun bayanai da ake buƙata don samun nasarar fara aiwatar da shirin a Jahar Zamfara ga Ofishin Bankin Duniya dake Abuja.
Hajiya Sa'adatu Abdu Gusau ta bayyana cewa, bayan amincewa da biyan kuɗin tallafin fara shirin da Gwamna Dauda Lawal ya yi, tuni har an biya kuɗaɗen ba tare da ɓata lokaci ba.
Ta kuma ƙara da cewa, a baya Jahar Zamfara ta yi ta kuskuren samun irin waɗannan tallafi na bunƙasa ilimi, to amma a halin yanzu Sabon Gwamnan Jahar Dr. Dauda Lawal ya yi alƙawarin bata dukkan taimako da haɗin kai da ake buƙata wajen samun nasarar aiwatar da shirin a Jahar.
Hajiya Sa'adatu Abdu Gusau ta jaddada cewa, a ƙarƙashin wannan sabon shiri na (AGILE AF Project-Zamfara) za a gina tare da gyara Makarantu da dama a Jahar Zamfara sa'annan kuma za a samar da Fasahar Zamani ga Ɗalibai ƙari ga Tallafin Kuɗaɗe ga Ƴaƴa Mata da Maga'isansu da kuma sauran abubuwan amfani masu yawa dake ƙarƙashin shirin.
Daga ƙarshe, Hajiya Sa'adatu Abdu Gusau ta roƙi ɗaukacin al'ummar Jahar Zamfara da su mara wa Gwamna Dauda Lawal da kuma shirin na (AGILE AF Project-Zamfara) baya domin cigaban Ilimin Ƴaƴa Mata a Jahar Zamfara.
Very good
ReplyDelete