Jami'an yansanda sunkai samame Gidan Tsohon gwmnan
Hakan na zuwa ne bayan da rahotanni suka bayyana cewa jami'an tsaro sun yi dirar mikiya a gidajen tsohon gwamnan da ke Gusau, babban birnin jihar da kuma a Maradun.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta hannun mai taimaka wa gwamnan, Dauda Lawal kan harkar yaɗa labaru, Sulaiman Bala Idris, ta ce an kai samamem ne bayan samun izini daga kotu.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin jihar ta zargi Bello Matawalle da tafiya da wasu kayan gwamnati, ciki har da motocin alfarma na gwamnati bayan saukar sa daga mulki.
Tuni dai tsohon gwamnan ya musanta zarge-zargen.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ƙara da cewa cikin motocin da aka gano daga gidan tsohon gwamnan akwai motoci masu sulke guda uku da kuma manyan motoci na SUV guda takwas.
An dai fara takun-saƙa tsakanin toshon gwamna Bello Matawalle da sabon gwamna Dauda Lawal ne tun gabanin miƙa mulki.
Dauda Lawal na jam'iyyar PDP shi ne ya kayar da Bello Matawalle na APC a zaɓen gwamna da ya gabata, inda adawa ta yi matuƙar zafi.
Comments
Post a Comment