Chukwu Obakalu ya rubuta takardar buƙatar horas da sojoji masu busa badujala na sojojin ƙasa da na sama
Jagoran masu busa, Chukwu Oba Kalu na kokarin ganin fatan da yake da shi kan salon busa na bagpipe tun yana karami ya samu karbuwa. Mai shekara 46, Chukwu ya fara ganin ana amfani da abin busa na bagpipe ne tun lokacin yana da shekara 18, lokacin yana cikin kungiyar Boys Brigade a jihar Abia, da ke gabashin Najeriya. Abin ya burge shi, kuma ya sha alwashin cewa zai koyi yadda ake yin irin wannan busa. "Sautinta ya yi daban da saura. Sautinta na da kayatarwa...yana taɓa zuciya," kamar yadda ya shaida wa BBC. A farko ya yi yunƙurin shiga Cibiyar koyar da badujala ta ƙasar Scotland, to amma ba ya da kuɗin da zai yi hakan. Sai kuma ya yi ƙoƙarin ganin an kawo masa kakakin daga ƙasar waje, sai dai hakan ma ba abu ne mai sauƙi ba. Ya tura saƙonni zuwa ga masu sayar da kayan koyon badujalar a Birtaniya da Amurka, to amma bai samu martani ba na tsawon lokaci. ASALIN HOTON, CHUKWU OBA KALU Daga baya ya samu martani na farko, wanda hakan ya tabbatar masa da dalilin da ya sa bai samu ...