Tajuddeen da Akpabio sun samu nasar

 An zaɓi Sanata Godswill Akpabio, a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai ta goma a Najeriya, da kuma Sanata Barau Jibrin a zaman mataimakinsa.

Yayin da aka zaɓi Onarabul Tajuddeen Abbas da Onarabul Benjamin Kalu, a matsayin shugaba da mataimakin shugaban majalisar wakilai.

Godswill Akpabio ya ci zaɓen ne da ƙuri'a 63 a kan abokin takararsa Sanata Abdul'aziz Yari wanda ya samu ƙuri'a 46.

Daidai lokacin da 'yan majalisar wakilai 353 suka kaɗa ƙuri'unsu ga Tajuddeen Abbas, wanda ya zama shugaban majalisar wakilai.

SAMSUNG Galaxy S22 Ultra Cell Phone, Factory Unlocked Android Smartphone, 256GB, 8K Camera, Brightest Display Screen, S Pen, Long Battery Life, Fast 4nm Processor, US Version, 2022, Phantom Black  https://amzn.to/3N3Skue

Amazon is selling the unlocked Samsung Galaxy S22 Ultra at its lowest ever prices in all storage configurations and multiple color options...

a kayar da tsohon mataimakin shugaban majalisar, Onarabul Idris Ahmed Wase da kuma Aminu Sani Jaji, inda kowannensu ya samu ƙuri'a uku.

Sanata Barau Jibrin ya ci zaɓe a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai ne ba tare da hamayya ba. Haka shi ma Ben Kalu a majalisar wakilai.

Sabbin shugabannin majalisar ta goma su ne suka samu goyon bayan jam'iyya mai mulki ta Najeriya wato APC da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Akawun majalisar tarayya, Sani Tambuwal tuni ya rantsar da su, inda suka hau kan kujerun shugabanci kafin a ci gaba da rantsar da sauran zaɓaɓɓun 'yan majalisar.

Comments

Popular posts from this blog

Introduction Microsoft Word

What is Shortcuts